
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta bayyana cewa dalibai 92 da ke da matsalolin gani ne suka halarci jarabawar UTME ta bana a cibiyar Kano da ke karkashin shirin JEOG na musamman ga masu bukata ta musamman.
Shugaban cibiyar JAMB ta Kano, Farfesa Muhammad Yahuza-Bello, ne ya bayyana hakan yayin da yake sa ido a lokacin gudanar da jarrabawar ranar Litinin a makarantar School of Continuing Education da ke Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).
Yahuza-Bello, wanda tsohon shugaba ne na Jami’ar BUK, ya ce daliban sun fito ne daga jahohin Kano, Jigawa, Katsina, Zamfara da Kaduna. Ya kuma kara da cewa a cikin wadanda suka rubuta jarrabawar, akwai guda biyu da ke da cutar Down syndrome da wasu biyu masu cutar autism.
An samar wa daliban kayan aiki na musamman kamar na’urar buga rubutu (typewriters), na’urar Braille, slates, styluses da takardu domin saukaka musu gudanar da jarrabawar.
Yahuza-Bello ya ce fiye da dalibai 500 masu bukata ta musamman daga sassa daban-daban na Najeriya sun yi rajista domin rubuta jarrabawar a wurare 11 da aka tanada a fadin kasa.
Ya ce sabanin cibiyoyin CBT na gama-gari inda ake amfani da allo da maɓalli, daliban da ke da bukatu na musamman suna amfani da kayan da aka daidaita domin kau da cikas ga samun ilimi.
Tun bayan kirkiro shirin JEOG a shekarar 2017, Farfesa Yahuza-Bello ya ce akwai gagarumin ci gaba, inda ya bayyana cewa kimanin kaso 33 cikin 100 na daliban da ke da bukata ta musamman ke samun guraben karatu a jami’o’i, sabanin kaso 25 cikin 100 na daliban gama-gari.